Gerrard ya ce yana da zabin yin wasa a LA Galaxy

Liverpool

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Gerrard tsohon dan kwallon Liverpool ya ce zai bar murza-leda a kungiyar LA Galaxy

Tsohon dan kwallon Liverpool, Steven Gerrard, ya ce yana da zabin lokacin da ya kamata ya buga wasa ko kuma ya hutu, bayan da ya ce zai bar LA Galaxy mai buga gasar Amurka.

Gerrard mai shekara 36, ya koma Galaxy a shekarar 2015, ya kuma ci kwallaye biyar a wasanni 34 da ya buga a kakar wasanni biyu.

Dan wasan ya ce zai bar Galaxy ne kwana daya tsakani bayan da Frank Lampard ya ce ya kusa ya bar kungiyar New York City wadda yake buga wa wasanni.

Gerrard ya yi wa Liverpool wasanni 710 a tsakanin 1998 zuwa 2015, kuma da zarar an rufe kakar wasannin kwallon kafa ta Amurka, ya kan yi atisaye ne a filin Melwood na Liverpool.