Kada kuri'arka a wannan shafi

Pierre-Emerick Aubameyang, da Andre Ayew, da Riyad Mahrez, da Sadio Mane da kuma Yaya Toure
Bayanan hoto,

'Yan takarar Zakaran Kwallon Afirka na BBC na 2016

'Yan takarar Zakaran Kwallon Afirka na BBC na 2016, sun hada da Pierre-Emerick Aubameyang, da Andre Ayew, da Riyad Mahrez, da Sadio Mane da kuma Yaya Toure.

Latsa wannan shafi domin kada kuri'a kan gwarzon da ka ke so a cikin wadannan 'yan wasa biyar.

Ranar Litinin, 12 ga watan Disamba ne za a bayyana sunan wanda ya lashe kyautar kai-tsaye a BBC Focus on Africa talabijin da rediyo. Mu ma a Sashen Hausa za mu ba da sanarwar kai-tsaye a shafin mu na BBC Hausa Facebook.

Shafin mu kuma na bbchausa.com ma zai dauki sanarwar gwarzon da ya lashe kyautar. Za ku iya duba ka'idojin zaben anan.