Nigeria: Matasa sun toshe kofar shiga Majalisa Dokoki

Matasa sun yi zanga-zanga a kofar Majalisar Dokokin Najeriya
Bayanan hoto,

Masu zanga-zangar na rike da kwalaye da rubuce-rubuce, da ke bayyana kyamar cin hanci da rashawa

A Najeriya, wasu kungiyoyin matasa sun rufe kofar shiga majalisar dokokin kasar, suna cewa ba za su gusa ba sai `yan majalisar sun sauya halayensu, sun bi sahu a yakin da gwamnatin kasar ke yi da cin hanci da rashawa. Matasan dai na zargin cewa babu abin da `yan Majalisar suka sa a gaba face son zuciya, lamarin da suka ce ba zai haifar wa Najeriya alheri ba.

Matasan, wadanda suka yi gangami a mashigar Majalisar dokokin Najeriyar sun ce sun dauki wannan matakin ne don nuna goyon bayansu ga aniyar shugaba Buhari, ta yaki da cin hanci da rashawa, yakin da suka ce wajibi dukkan masu kishin kasar su shiga tafiyar.

A cewarsu sai da suka tsaya suka yi nazarin dabi`un `yan Majalisar dokokin Najeriya, kafin su kai ga zanga-zangar tasu ta zaman dirshan, amma sun fahimci cewa, kamar yadda suke zargi ba kishin kasa ba ne a gaban `yan Majalisar.

Bayanan hoto,

Gangamin matasan dai ya samu halartar wasu daga fitattun masu fafutika, ciki har da sanannen mawakin nan Charley Boy

Gangamin matasan dai ya samu halartar wasu daga fitattun masu fafutika, ciki har da sanannen mawakin nan Charley Boy.

Charley Boy kuma ya yi bayanin cewa, " Na hanga cewa ya kamata matasa su taka rawar da ta dace da su a tsakanin al`uma. Don haka na zo wannan wurin ne domin nuna musu goyon baya".

Kokarin BBC na jin ta bakin shugabannin Majalisar dokokin Najeriyar, dangane da wannan matsayi na masu zanga-zangar, bai yi nasara ba.

Sai dai wasu daga cikin `yan majalisar sun ce ana jahiltarsu ne kawai, amma dukkansu manufarsu guda.

Bayanan hoto,

Matasan sun ce suna goyon bayan yakin da shugaba Buhari ke yi da cin hanci da rashawa

A `yan makwannin baya dai wasu matasan sun yi irin wannan zanga-zangar zaman-dirshan din, amma za a iya cewa ba su yi wani tasirin azo-a-gani a Majalisar ba.

Ana dai duba yiwuwar ko sabon yunkurin nan, zai kai labari a wannan karon.

Bayanan hoto,

Sakon kyallen na cewa tunda kudin shigar kasar ta ragu, to dole albashin jami'an gwamnati ma ya ragu