Shugaban Rasha Vladimir Putin ya kori minista daga aiki

Shugaba Putin ya ce ministan ya bashi mamaki bisa abinda ya aikata
Shugaba Putin na Rasha ya kori ministan bunkasa tattalin arzukinsa Alexei Ulyu-kayev, wanda aka tuhuma da karbar cin hancin dala miliyan biyu.
Kakakin Mr Putin Dmitri Peskov, ya ce shugaban ya daina amincewa da Mr Ulyu-kayev, wanda ya musanta zarge zargen.
Shi ne dai ministan Rasha na farko da aka kama cikin shekaru ashirin da biyar.
Firaministan Rashan, Dmitry Medvedev, ya kwatanta lamarin a matsayin wani mai wuya ga gwamnati wanda ya kasa gane masa.