An kai hari filin jirgin saman Oklahoma na kasar Amurka

An rufe filin jirgin saman saboda harin da aka kai
An rufe filin jirgin saman birnin Oklahoma na kasar Amurka sakamakon harbe-harbe da aka yi a ciki lamarin da ya yi sanadiyyar rasa ran mutum guda.
An kuma rufe dukkan wasu hanyoyi, kana an shaidawa fasinjoji da kada su kusanci filin jirgin saman.
Wadanda ke ciki kuwa an umarce su da su nemi mafaka a ciki.
'Yan sanda sun ce suna neman wani da ba mamaki harbin ya same shi.