Donald Trump abokin tafiyarmu ne - Assad

Bashar Al-assad

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Assad dai na fata Amurka za ta daina katsalandan cikin al'amurran wasu kasashe a karkashin Mr. Trump

A kalamansa na farko kan manufofin Amurka tun bayan zaben Donald Trump, Shugaban Syria Bashar Al - assad ya ce shugaban mai-jiran-gado ka iya zama abokin tafiya ga kasarsa wajen yaki da ta'addaci.

Sai dai shugaban na Syria ya ce zai jira ne ya ga kamun ludayin Mr. Trump in har zai iya cika alkawarin da ya yi na yakar ta'addanci kasancewar bai taba rike mukaminsa siyasa ba a baya.

''A wurinmu dai har yanzu abin na a cikin duhu na ko zai iya cika alkawurran da ya yi ko kuma a'a. Wannan ne ya sa muke kafa-kafa wajen daukar wata matsaya a kansa musamman saboda bai taba rike mukamin siyasa ba a baya. ''

Shugaba Assad ya ce kodayake ba zai ce komai ba tukuna kan ko shugaban mai-jiran-gado zai iya kawo sauyi a manufar Amurka kan kasarsa , yana fatan Amurka ta kasance ''mai adalci, da mutunta dokokin kasa da kasa, kuma bugu da kari ta daina mara wa 'yan ta'adda baya a Syria.''

A lokacin yakin neman zaben sa dai Donald Trump ya sha alwashin ruguza kungiyar IS, yayin da ya yi Allah-wadai da manufar gwamnatin Obama ta mara wa 'yan tawayen na Syria baya.