Messi da tawagarsa sun yi wa 'yan jarida bore

Lavezzi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

An zargi Lavezzi da shan wiwi

Lionel Messi ya jagoranci 'yan wasan Argentina domin kin yin hira da 'yan jarida saboda rahotanni "marasa dadi" da suka wallafa a kan tawagar kwallon kafar kasar.

Dan wasan mai shekara 29 ya bayyana cewa ba za su yi hira da 'yan jarida ba bayan an kammala wasan cancantar shiga gasar cin kofin duniya inda suka doke Colombia da 3-0.

Wani rahoto da 'yan jarida suka wallafa ya yi zargin cewa dan wasan gaba Ezequiel Lavezzi ya sha tabar wiwi bayan sun yi atisaye, kodayake ya musanta zargin.

Messi ya ce, "Mun sha suka daga wajen 'yan jarida, kuma yawancin abubuwan da ake fada a kan mu na rashin da'a ne amma ba mu ce komai ba."

Messi da sauran 'yan wasan 25 sun yi banza da 'yan jarida bayan an kammala wasan.

An bayyana cewa Lavezzi zai kai gurfanar da dan jaridar da ya zarge shi da shan wiwi a kotu.