'Yan Niger Delta Avengers sun sake fasa bututan mai

Mayakan sun ce ba su amince da aniyar gwamnatin Buhari ba

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Mayakan sun ce ba su amince da aniyar gwamnatin Buhari ba

Rahotanni daga Najeriya na cewa mayakan yankin Naija Delta sun sake fasa bututan mai guda uku a yankin.

Kamfanin dillancin labarai na AP da AFP sun ambato mazauna yankin na cewa an fasa bututan man ne da ke da tazarar kilomita 100 tsakaninsu ranar Talata da daddare.

Wannan dai shi ne karo na biyar da mayakan ke fasa bututan man a cikin wata daya duk da tayin sulhun da Shugaba Muhammadu Buhari na kasar ya yi musu.

Kungiyar Niger Delta Avengers ta ce ta kai hari a kan bututan da ke daukar gangar mai 300,000 daga Nembe zuwa tashar Bonny wacce kamfanin Shell ya mallaka.

Wani shugaban yankin Stephen Igwe ya ce an kai hare-hare a kan bututan mai na Tebidaba-Brass mallakin kamfanin Agip.

A farkon watan nan ne mayakan suka kai hare-hare kan tashar Trans Forcados.

Sun yi zargin cewa ba da gaske gwamnati take ba a kokarin da take yi na ci gaban yankin.