Ana zargi wani gwamna da yin saɓo a Indonesia

Masu zanga-zanga sun zargi gwamnan da yin ɓatanci ga Al-Qur'ani

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Masu zanga-zanga sun zargi gwamnan da yin ɓatanci ga Al-Qur'ani

'Yan sandan kasar Indonesia sun bayyana cewa gwamnan Jakarta, Basuki Tjahaja Purnama, na cikin mutanen da suke zargi da yin saɓo.

An zargin gwamna Purnama, wanda aka fi sani da suna "Ahok", da laifin wulakanta ayoyin Al-Qur'ani a lokacin da yake yakin neman zabe.

Purnama, wanda Kirista ne, shi ne dan kabilar China na farko da ya zama gwamna a kasar da mafi yawan mutanenta Musulmi ne.

Sanya sunan sa a cikin wadanda ake zargi da yin saɓo na nufin za a iya tuhumarsa a gaban kotu.

Idan kuma aka kama shi da laifi zai iya fuskantar daurin shekara biyar a gidan yari.

Mr Purnama na shirin sake tsayawa takara a watan Fabrairu na shekarar 2017.

A kwanakin baya ne aka yi zarga-zanga kan zargin gwannan da yin ɓatanci ga Al-Qur'ani.

Masu zanga-zangar sun ce bai kamata ya rika amfani da ayoyin Al-Qur'ani wajen yakin neman zabe ba.