An kira Michelle Obama biranya

Asalin hoton, Getty Images
Michellle Obama ce bakar fata ta farko da zama matar shugabar Amurka
Wata shugabar birni ta yi murabus a jihar West Virginia da ke Amurka bayan ta kwatanta matar Obama, Michelle Obama da biranya.
Beverly Whaling dai ta yaba wa wani sako da aka wallafa a shafin facebook inda aka bayyana Mrs Obama a matsayin "biranya sanye da takalmi mai tsayi"
Ta rubuta cewa sakon da aka wallafa ya sa ta ji dadin ranar, amma kuma daga baya sai ta mayar da martani kan sakamakon zaben Amurka.
Mutum 170,000 ne dai suka sanya hannu a wani korafi inda suka bukaci shugabar birnin ta yi murabus.
Ms Whaling ce dai shugabar birnin Clay, wanda ke da yawan mutane 491 kafin ta yi murabus.
A cewar kididdigar shekarar 2010, garin ba shi da mazauna, Amurkawa 'yan asalin Afirka.
A baki daya garin Clay, sama da kashi 98 cikin 100 na mazauna su 9,000 da garin Turawa ne.