Mutmin da yafi kowa kiba a duniya na kwance a asibiti

Juan Pedro Franco

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Franco na kokarin ya rage kilogram 45 na nauyinsa kafin a yi masa tiyata

An kwantar da mutumin da ya fi kowa nauyi a duniya, Juan Pedro Franco, a asibiti bayan da ya kasa tafiya saboda nauyinsa ya kai sama da kilogram 500.

Mista Pedra, mai shekara 32 ya kwashe mafi yawan lokuta a shekara 15 da yayi a cikin wani karamin gado a gidansa da ke birnin Aguascalientes na Mexico.

Kibarsa ta karu ne bayan ya kamu da cutar nimoniya da hatsarin da ya yi a lokacin da yana matashi lamarin da yasa shi jin jinyar sama da shekara guda.

Ya kara nauyi sama da kilogram 95 a cikin watanni hudu kawai tun bayan da ya nemi taimakon kudi domin ya sauya irin abincin da ya ke ci.

Dakta Jose Antonio Castaneda Cruz, na daga cikin tawagar likitocin da za su kula da Mista Pedro a asibitin Jardines da ke Guadalajara.

Ana bukatar ya rage kilogram 45 na nauyinsa kafin a yi masa tiyata.

Matsananciyar tebar da yake da ita ta sa mai yiwu wa ya doke dan kasar Mexico Manuel Uribe, a matsayin mtumin da ya fi kowa nauyi a duniya.

Mista Uribe, mai shekara 48, ya mutu yana da nauyin kusan kilogram 600 a shekarar 2014.

An yi amfani da na'urori na musamman wajen daukar Juan Pedro ciki har da ta taimakawa wajen yin numfashi kafin a kai shi asibiti.

Mista Pedro, mai buga na'urar jita ya nemi taimako a watan Yuli a lokacin da nauyinsa ya haura kilogram 381, inda ya bayyana cewa ya shafe shekara shida bai bar dankisa ba bayan ya bar cin abinci na mussaman lokacin da iyayensa 'yan fansho suka kasa saya masa.