Mace ta dauki ciki sau biyu cikin kwana 10

'Yan biyu Charlotte da Olivia

Asalin hoton, SEVEN NETWORK

Bayanan hoto,

Yana da wuya dai ciki ya sake shiga mahaifa, bayan ta riga ta dauki cikin farko.

Wata mata 'yar kasar Australiya da likitoci suka ce baza ta haihu ba, ta ce ta dauki ciki sau biyu da ke kwanaki goma tsakanin samun su.

Matar mai suna, Kate Hill na shan magungunan gyara kwayoyin halitta ne, bayan da likitoci suka gane cewa tana wata cuta ta mahaifa, watau Polycystic Ovary Syndrome, ciwon da ya hana ta daukar ciki.

Bayanai dai sun nuna cewa ta samu cikin 'yan biyun ne a lokuta daban-daban, duk da cewa sau daya ne kacal ta yi jima'i ba tare da amfani da hanyar takaita haihuwa ba, watau roba.

Yana da wuya dai ciki ya sake shiga mahaifa, bayan ta riga ta dauki cikin farko.

'Yan biyu dai mafi yawancin lokuta, ana samun su ne sakamakon fitar da kwayaye biyu a lokaci guda, ko kuma idan kwai guda ya rabe biyu a mahaifa.

An haifi mata 'yan biyun, Charlotte da Olivia, watanni goma da suka gabata, inda rahotanni ke cewa, suna da nauyi daban-daban da kuma watannin haihuwa daban-daban.

Asalin hoton, SEVEN NETWORK

Bayanan hoto,

"Bamu gane muhimmancin abin da ya faru ba, sai bayan haihuwarsu."

Misis Hill dai ta shaida wa gidan talabijan din Australiya, Seven Network, cewa;

"Bamu gane muhimmancin abin da ya faru ba, sai bayan haihuwarsu."

Ciki dama yana tsayar da jinin al'ada, amma ba a cika samun yanayin da mace ke sake fitar da wani kwan kuma a mahaifarta ba, bayan tana da wani cikin.

Idan dai hakan ya faru, to kwan zai iya girma ta kuma haihu lafiya.

Ana dai da labarin makamancin wannan abun al'ajabi guda goma ne kawai, wadanda suka afku a baya.

Likitan ma'auratan dai ya ce lamarin ba kasafai yake afkuwa ba, kuma sai da ya tilasta masa yin bincike kan sa a shafin intanet.

Ya ce, "Ban samu wani darasi kan sa ba a litattafen mu na likitoci, da ma wasu shafukan likitoci a intanet.