Rikicin Myanmar: Mutane arcewa zuwa Bangladesh

Musulmai 'yan kabilar Rohinjya na tserewa rikicin Rakhine
Bayanan hoto,

Musulmai 'yan kabilar Rohinjya na tserewa rikicin Rakhine

Daruruwan musulmai 'yan kabilar Rohingya da suka hada da kananan yara na ta kokarin tserewa rikicin da ake a Myanmar ta hanyar tsallaka kan iyakar Bangladesh.

Farmakin da sojoji suka kai a jahar Rakhine ta Myanmar din, inda da yawan 'yan tsiraru 'yan kabilar Rohingya ke zama, ya halaka a kalla mutane dari da talatin a cikin wata guda.

Masu fafutuka da shaidu sun ce an kona daruruwan gidaje kurmus.

Gwamnatin kasar Burma ta musanta ikirarin, amma kuma sun ki yadda 'yan jarida na kasashen waje su je wajan.

Shaidu da jami'an Bangladesh sun ce an harbe har lahira wasu da suka yi kokarin tserewa zuwa Bangladesh, yayin da aka tilastawa wasu kuma komawa gida.