Jiragen ruwan Netherland uku sun nitse a tekun Java na kasar Indonesia

Jiragen ruwan sun nitse ne a lokacin yakin duniya na biyu
Gwamnatin Birtaniya ta ce ta damu da wani rahoto da ke cewa wasu jiragen ruwa da suka nitse a lokacin yakin duniya na biyu, sun bace ne daga kasan tekun Java.
Netherland ta tabbatar da cewa jiragen ta uku da suka nitse wanda ta kira da kaburburan mutanensu na bangaren mazan jiya, sun bace ne tun daga wajen da ke gabar tekun Java a Indonesiya.
Ana tunanin cewa an yi dai-dai da jiragen ne domin amfani da karafunansu.
Ma'aikatar tsaron Jamus ta ce lalata kaburburan sojojin da suka mutu a fagen daga, babban laifi ne.
Sojojin ruwan Indonesiya sun ce za su yi bincike akan wannan batu.