Birnin New York na cikin tsoron mulkin Trump - Blasio

Asalin hoton, AP
Donald Trump dai ya tashi ne a birnin New York kuma har yanzu shi ne gida na farko a gare shi.
Magajin garin birnin New York Bill De Blasio ya ce ya fada wa Donald Trump cewa al'umomin baki da ke birnin na cikin fargabar abin da zamansa shugaban kasa zai jawo musu.
Bayan wani taro wanda ya kira na fada wa juna gaskiya, Mr. Blasio dan jam'iyyar Demokrat, ya ce ya nuna wa Mr. Trump cewa iyalai masu dimbin yawa za su tarwatse sakamakon shirinsa na tasa keyar baki zuwa kasashensu.
Bayan da ya ci zabe dai Mr. Trump sai ya ce babban abin da yake shirin yi shi ne kau da ko tsare kimanin bakin haure miliyan uku wadanda ke tarihin aikata wani laifi.
Sai dai tuni jami'an manyan biranen Amurka suka nuna rashin amincewa da wannan shawarar tasa, sai kuma yanzu magajin garin birnin na New York, ya ce birnin zai yi duk iya abin da zai iya domin kare ma'aikatan da ba su da takardun iznin zama kasar da ke zaune a can daga a tasa keyarsu zuwa kasashensu.
Birnin na New York na da kusan ninki uku sama ga adadin bakin aka kayyade kowane birni a kasar ya tsugunar kuma a baya Mr. De Blasio ya sha alwashin goge sunaye ma'aikatan da ba su da takardun iznin zama kasa daga naurorin adana bayanai, domin hana a zakulo su.