'An buga hotunan Wayne Rooney ya yi mankas da giya'

Rooney

Asalin hoton, Rex Features

Bayanan hoto,

Rooney ya nemi gafara

Kyaftin din Ingila Wayne Rooney ya nemi afuwar kocin tawagar kwallon kafar kasar na riko Gareth Southgate bayan an fitar da wasu hotuna da ke nuna shi a wajen wani biki a otal din da tawagar kasar ke zaune.

Wata sanarwa da aka fitar a madadinsa ta ce Rooney, mai shekara 31, ya amince cewa hotunan ba su dace ba.

Jaridar The Sun ta wallafa hotunan da ta ce sun nuna Rooney ya bugu da giya a wajen wani biki da tsakar daren ranar Asabar - kwana daya bayan Ingila ta doke Scotland a wasan cancantar shiga gasar cin kofin duniya.

A waje guda kuma, hukumar kwallon kafar Ingila, FA, ta ce tana duba yiwuwar yin sauye-sauye ga dokar barin 'yan wasa suna amfani da lokutan hutunsu.

Jaridar The Sun ta ce FA za ta yi sauye-sauyen ne saboda 10 daga cikin 'yan wasan Ingila sun tafi gidan sharholiya inda suka kai har karfe 04:30 na asubahin ranar Lahadi bayan wasan da suka yi.