Sakamakon zaben Amurka ya gigita ni - Clinton

Clinton

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Clinton ta bukaci Amurkawa kada su karaya

A karon farko Hillary Clinton ta fito fili ta bayyana irin takaicinta a kan shan kayen da ta yi a hannun Donald Trump a zaben kasar da aka yi a makon jiya.

Misis Clinton ta ce sai da ta ji kamar ta hada kanta da gwiwarta ta rufe a cikin wani "littafi sannan na ki fitowa daga gida har abada".

Sai dai a wani jawabi da ta yi a wurin wata gidauniyar yara marasa galihu, Misis Clinton ta yi kira ga mahalarta taron da su zage dantse domin yaki wajen kare martabar muradun Amurka kuma kada su taba karaya.

'Yar takarar jam'iyyar Democrat din dai ita ce ta lashe yawancin kuri'un da aka kada a zaben, sai dai Mista Trump ya fi ta yawan wakilan da suke zabar shugaban kasar, abin da ya sa ya yi nasara.

Misis Clinton ta shaida wa mahalarta taron cewa, "A gaskiya zan fada muku cewa ba na yi kokari sosai kafin na iya zuwa nan. Na san yawancin ku ba ku ji dadin sakamakon zaben ba. Ni ma ban ji ba, fiye da yadda kuke tsammani

"Na san hakan na da matukar wuya. Na san cewa mutane da dama sun kashe tsawon wannan mako suna tambayar cewa anya wannan ita ce kasar Amurkan da muke tunani."

Mahalarta taron sun yi ta jinjina mata, suna masu cewa gwiwoyinsu ba su yi sanyi ba.