Amurkawa na fama da jarabar shan miyagun kwayoyi

Murthy ya ce ya zama wajibi a dauki mataki

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Murthy ya ce ya zama wajibi a dauki mataki

Shugaban kiwon lafiyar al'uma na Amurka ya yi kira dauki matakin gaggawa domin magance matsalar jarabar shan miyagun kwayoyi da barasa.

Vivek Murthy ya ce shan miyagun kwayoyi da barasa na daya daga cikin matsaloli mafiya tsanani a wannan zamani.

A cikin wani rahoto na farko irinsa, Vivek Murthy, ya ce shan miyagun kwayoyi na shafar muliyoyin Amurkawa, da kuma janyo asara ta $50000m a kowace shekara.

A cewarsa, duk da wannan matsalar, mutum daya ne kacal cikin goma ke yin jinya.

Admiral Murthy ya jaddada cewa akwai bukatar a sauya baki dayan yadda ake tunkarar lamarin, yana mai cewa maimakon a rika daukar shan miyagun kwayoyi a matsayin matsalar lalacewar tarbiya, ya kamata a rika kallon lamarin a matsayin wata mummunar cuta tamkar sankara ko ciwon sukari.