Mutum da ya cinna wa kansa wuta a Australia

Wutar ta kona na'urar cirar kudi

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Wutar ta kona na'urar cirar kudi

Wani mutum a kasar Australia ya shiga wani banki a birnin Melbourne, sannan ya cinna wa kansa wuta lamarin da ya kai ga kona mutum 26, in ji 'yan sandan birnin.

Sun kara da cewa shida daga cikin mutanen na cikin mawuyacin hali, yayin da wasunsu suka kone kadan tare da shakar iskar guba, cikin su har da kananan yara.

'Yan sandan sun ce mutumin da ake zargi da banka wutar ya shiga wani reshen bankin Commonwealth da ke Springvale sannan ya yi amfani da fetur wajen tayar da wutar.

An kai mutumin asibiti domin yi masa magani, kodayake 'yan sanda suna sanya masa ido.

Wata mai rikon mukamin Sufeto Jackie Poida ta shaida wa manema labarai cewa mutumin mai shekara 21 na dauke da abin da ke saurin sanya wuta ta tashi a lokacin da ya shiga bankin.

Ta kara da cewa ya yi wuri a san dalilin da ya sa mutumin ya cinna wa kansa wuta.