An zartar da hukuncin kisa kan dan Nigeria a Singapore

An yi kokarin hana kashe su

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

An yi kokarin hana kashe su

Hukumomi a kasar Singapore sun ce sun kashe mutum biyu - dan Najeriya da dan Malaysia - bayan sun kama su da laifin yin safarar miyagun kwayoyi.

Wata sanarwa da hukumar da ke yaki da safarar miyagun kwayoyi ta kasar ta fitar ta ce an kashe Chijioke Stephen Obioha a gidan yarin Changi ranar Juma'a.

Ta kara da cewa an same shi ne da laifin yin safarar tabar wiwi mai nauyin giram 2,604.56 a shekarar 2008.

Shi kuma dan kasar Malaysia, Devendran Supramaniam, ya shiga hannun jami'an tsaro ne a shekarar 2011 saboda yunkurin shiga kasar da hodar ibilis mai nauyin gram 83.36.

Lauyan Obioha da kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International dai sun yi ta fafutikar ganin ba a aiwatar da hukuncin kisa a kansa ba.

Dokokin kasar Singapore sun amince a kashe duk mutumin da aka kama da fiye da gram 500 na wiwi.