Za a yi wa Gareth Southgate gwaji

Gareth Southgate

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Gareth Southgate ya lallasa Scotland da Malta, sannan ya yi kunnen-doki da da Slovenia

Gareth Southgate zai gana da jami'an hukumar kwallon kafar Ingila ranar Litinin domin yi masa tambayoyi kan yiwuwar tabbatar masa da mukamin kocin Ingila.

Southgate, mai shekara 46, bai dade da kammala wasa hudu a matsayin kocin riko bayan an kori Sam Allardyce.

Wadanda za su yi masa gwaji a filin wasa na St George's Park sun hada da shugaban hukumar gudanarwa ta FA, Greg Clarke, da shugaban FA Martin Glenn, mai kula da harkokin wasanni Dan Ashworth, da shugaban lig Howard Wilkinson da kuma tsohon dan wasan baya na Ingili Graeme Le Saux.

FA ta dage cewa ba ta ware ranar da za ta nada kocin dindindin ba, a yayin da kasar ke shirin buga wasan sada zumunta da Jamus a watan Maris, kuma Clarke, Glenn da Ashworth ne za su dauki mataki na karshe kan tabbatar da mukamin kocin.

Hukumar ta ce tana yin aiki a nutse ne kafin nada kocin na dindindin, tana mai cewa babu wanda zai azalzale ta kodayake ana ganin Southgate ne ya fi dacewa ya zama kocin.