Nigeria:`Yan sanda na binciken bidiyon kisan-gilla

'Yan sandan Najeriya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

An yi ta yi wa yaron duka da jifa kuma aka cinna masa wuta

Rundunar `yan sandan Najeriya ta fara gudanar da bincike don gano gaskiyar kisan-gillar da aka yi wa wani yaro da ake zargi da satar abinci, bayan yayata hoton bidiyon kisan ta kafafen sadarwa na zamani.

Alamu dai na nuna cew an dauki hoton bidiyon ne a Lagos, inda wasu bata-gari ke magana cikin Yarbanci da Ingilishin Pidgin (broka), harshen da galibin jama`a ke magana da shi a birnin.

Sai dai mai magana da yawun rundunar `yan sandan jihar Lagos, Dolapo Badmus ta shaida wa manema labarai cewa suna kokwanto ko al`amarin ya auku a Lagos, kana ta bukaci duk wani mai bayanin da zai taimaka wajen gano wadanda suka yi wannan aika-aikar, da ya tuntubi rundunar.

Ana dai takaddama a kan shekarun yaron da aka kashe, kasancewar wasu na cewa dan shekara bakwai ne da haihuwa, yayin da wasu kuma ke cewa matashi ne dan shekara 20 da doriya.

A cikin hoton bidiyon ana iya ganin dandazon jama`ar da ta kewaye yaron, wanda ake zarginsa da satar garin kwaki a wani shago.

Cikin hotunan har da inda aka yi wa yaron duka, aka yi ta jifar sa, kana aka daure shi sannan aka cinna masa wuta, lamarin da ya yi masa sanadin mutuwa.

Wannan lamari dai ya yi matukar bakanta ran `yan Najeriya, inda suka yi Allah-wadai, kana suka bukaci mahukunta da su kawo karshen irin wannan hukunci na mai-karfi-alkalin-kauye.