Japan za ta ci gaba da hulda da Amurka -Abe

Shinzo Abe tare da Donald Trump

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Mista Abe bai bayyana abubuwan da suka tattauna akai da Mista Trump ba

Shugaba Shinzo Abe na Japan ya gana da zababben shugaban Amurka Donald Trump, domin tattaunawa tare da fayyacewa kasar sa kalaman da Mista Trump ya yi amfani da su a lokacin yakin neman zabe.

Daga bisani bayan tattaunawar da shugabannin biyu suka shafe tsahon mintina casa'in, wadda aka yi ta a dogon ginin Trump Towers da ke Manhattan.

Shugaba Abe ya shaidawa manema labarai cewa tattaunawar da suka yi da Mista trump ta kara masa karfin gwiwa, kuma a shirye kasar sa ta ke dan kulla dangantaka mai dorewa tsakanin ta da Amurka.

Japan dai ta nuna damuwa matuka a lokacin da aka sanar da Mista Trump a matsayin sabon shugaban Amurka, saboda rashin sanin tabbas din ko kasashen biyu za su ci gaba da kasancewa kawaye musamman da fuskar huldar diplomasiyya da tsaro.

A lokacin da yake yakin neman zabe, mista Trump ya ce dole kasashe kawayen Amurka su shiga cikin taimakon da Amurka ke badawa, da suka hada da biyan dakarun kawance na NATO maimakon ita kadai ta dauki nauyin su.

A kuma wannan lokacin ya ce kamata ya yi Japan ta samar da makamin nukiliya na kashin kan ta, da kuma duba yiwuwar ci gaban kasashen biyu ta fuskar kasuwanci.

A ranar 20 ga watan junairu ne Mista Trump zai sha rantsuwar kama aiki, a kuma wannan ranar ne wa'adin mulkin shugaba Barack Obama ke zuwa karshe.