Tanzania: Likitoci sun gagara yi wa Elias aiki

Mista Elias ya ce ya na mamakin yadda mutane ke tururuwar zuwa kallon shi
Wani mutum dan asalin kasar Tanzani, ya shaidawa BBC cewa asibitin da ya ke ziyarta sun gagara yi masa aikin tiyata saboda tsahonsa.
Baraka Elias, mai tsaho kafa bakwai da inci hudu, ya ce ya na da lalura a kwankwasonsa saboda raunin da ya ji a lokacin da ya fadi, kuma ana bukatar ayi masa aikin gaggawa.
Likitocin da suke kula da lafiyar Mista Elias a babban asibitin kashi na gwamnati da ke Dar as-Salam, sun shaida masa cewa, tsahon da ya ke da shi ba zai bari ya kwanta salin-alin ba a gadon asibitin.
Haka kuma likitocin asibitin Muhimbili sun ce injin da ke daukar hoton jikin dan adam dan binciken kwakwaf ba a yi shi dan mutane dogaye kamar Mista Elias ba.
Labarin Mista Elias da ya fi kowa tsaho a baki dayan kasar Tanzania ya karade kafofin yada labaran kasar, inda mutane ke tururuwa dan ganewa idanun su.
Kowanne mutum ya zo babu abinda ya ke fata face ya tsaya kusa da Mista Elias inda za ka ga mutum ya yi dan kankani a gaban sa, wasu hotunan Internet da aka wallafa ya nuna yadda mutanen ke tsaye a kusa da shi.
Ya kara da cewa shi ya na mamakin yadda mutane ke al-ajabin tsahon shi, amma shi sam baya jin wani banbanci tsakanin sa da sauran mutane, kuma ya na gudanar da harkokin sa na yau da kullum kamar yadda kowanne dan adam ke yi.
Kasar Tanzania dai na daga cikin kasashe a nahiyar Afurka da bangaren kiwon lafiya ke cikin mawuyacin hali, tun daga kan kwararrun likitoci, har zuwa kan rashin kayan aiki.
To Amma likitoci sun tabbatar da cewa za a iya yi wa mista Elias aiki amma sai an dangana da kasashen turai.
Iyayen Mista Elias dai sun tabbatarwa da kamfanin dillancin labaran kasar cewa, tsahon na shi na gado ne.