Jami'an kasar Turkiyya na neman mafaka

Sojojin Turkiyya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Juyin mulkin Turkiyya ya jefa kasar cikin rikici a alummar

Sakatare Janar na kungiyar tsaro ta NATO ya ce jami'an kasar Turkiyya da dama, wadanda aka tura kungiyar tsaro ta Nato na neman mafaka tun lokacin da ba su samu nasara a yunkurin juyin mulkin kasar ba.

Jen Stoltenberg ya ce jami'an sun nemi mafaka a kasashen da aka tura su amma kuma ba su bayyana sunayensu da adadi da kuma dalilin bukatar tasu ba.

Kasashen da abin ya shafa za su duba lamarin.

Turkiyya dai ta sallama, tare da kora, da tsare ko kuma daure dubban mutane tun yunkurin juyin mulki da aka yi watan Yuli.

Da damansu sun yi aikin Soja, duk da dai cewa wasunsu malamai ne da 'yan sanda da alkalai da kuma 'yan jarida.

Gwamnatin Turkiyya na kai hari ne kan wadanda take zaton suna da alaka da Fethullah Gulen, mutumin da suka yi amannar ya jagoranci yunkurin juyin mulkin.