Amurka ta nuna damuwa kan kisan 'yan Shi'a a Nigeria

Amurka ta ce 'yan Shi'a na da 'yancin yin gangami

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Amurka ta ce 'yan Shi'a na da 'yancin yin gangami

Gwamnatin Amurka ta nuna damuwa game da asarar rayukan da ake yi a Najeriya, sakamakon arangama tsakanin `yan kungiyar `yan uwa musulmi da jami`an tsaro.

Wata sanarwa da ofishin jakadancin kasar da ke Najeriya ya fitar, ta ce akwai bukatar a dinga samun fahimtar juna tsakanin mabiya kungiyar da kuma mahukunta a Najeriya.

Amurka ta ce artabun da aka yi tsakanin `yan sanda da `yan Shi'a, wadanda ke tattaki daga Kano da nufin zuwa birnin Zazzau, a makon jiya, abin takaici ne.

Amurka ta ce hankalinta ya tashi matuka da irin karfin da `yan sanda suka yi amfani da shi a karawar, duk cewa mahukunta a Najeriya na ci gaba da gudanar da bincike a kan lamarin.

Gwamnatin Amurkar ta bukaci `yan kungiyar da kuma bangaren gwamnatin Najeriya da su kai zuciya nesa, tare da mai da hankali wajen tuntubar juna da nufin samun maslaha.

Sanarwar ta kara da cewa `yan kungiyar `yan uwa musulmi suna da `yancin yin taro da sauran hidimominsu na addini, kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadar, amma a bangare guda kuma wajibi ne su kasance masu martaba dokar kasar.

Gwamnatin Amurkar ta bukaci mahukunta a Najeriya da su gudanar da bincike na gaskiya da gaskiya a kan wannan sabon rikicin da kuma wani dauki-ba-dadin da sojoji suka yi da `yan kungiyar `yan uwa musulmin a watan Disamban bara, wanda ya yi sanadin mutuwar `yan kungiyar sama da 300.