An dakatar da ɗan wasan CSKA Moscow saboda shan ƙwaya

Ba zai dawo tamaula ba sai ranar shida ga watan Oktoba na 2018

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ba zai dawo tamaula ba sai ranar shida ga watan Oktoba na 2018

An dakatar da dan wasan CSKA Moscow Roman Eremenko daga kwallon kafa tsawon shekara biyu bayan an gano yana shan hodar ibilis.

An dakatar da dan wasan - mai shekara 29 - dan kasar Finland ne bayan wasan zakarun Turai da CSKA da Bayer Leverkusen suka tashi da ci 2-2 ranar 14 ga watan Satumba.

Shi ne ya ci wa CSKA kwallo ta biyu a wasan.

Yanzu dai ba zai dawo tamaula ba sai ranar shida ga watan Oktoba na shekarar 2018.

Wata sanarwa da Uefa ta fitar ta ce : "Binciken da aka yi a kan samfurin jininsa ya nuna cewa yana dauke da hodar ibilis da dangoginta."