Trump ya nada Jeff Sessions a matsayin Atoni Janar

Jeff Sessions da Zabebben shugaban Amurka, Donald Trump

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Jeff Sessions wani mai matukar goyon bayan Donlad Trump ne wajen gina katanga tsakanin Amurka da Mexico

Donald Trump ya bada wasu muhimman mukamai biyu ga wasu masu ra'ayin rikau a jam'iyyar Republicans.

Ya bukaci wani dan Majalisar dattawa daga Alabama, Jeff Sessions ya zamo Antoni Janar, yana mai bayyana shi a matsayin masanin shari'ah sahun farko a duniya.

Sai dai fa an taba kin amincewa da Mr Sessions, a matsayin alkali a kotun tarayya, a shekarun alif dari tara da tamanin, saboda furta wasu kalamai masu nasaba da wariyar launin fata.

Ron Christie, wani kusa ne a jam'iyyar Republican;

Ya ce,"Daga abin da na gani kuma na lura da shi, game da Jeff Sessions, ba mai nuna wariyar launin fata ba ne, ba shi da nuna bambanci."

Mr Trump ya kuma zabi Mike Pompeo wani dan Majalisar wakilai daga jihar Kansas, da ake dangantawa da kungiyar masu tsattsauran ra'ayi ta Tea Party, domin zama daraktan hukumar ayyukan leken asiri ta CIA.

Kafin haka yayi tayin bada mukamin mai bada shawara kan harkokin tsaro ga Michael Flynn wani tsohon Janar, da a kwanaki baya ya tura sakon twitter yana cewa akwai hujjar nuna dari-dari da musulmi.