Trump zai biya daliban jami'arsa miliyoyin daloli

Mista Donald Trump
Bayanan hoto,

A baya Mista Trump ya ce ba zai biya kudin ba

Zababben shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi amai ya lashe bayan da ya amince cewa zai biya miliyoyin daloli akan wata badakalar shari'a data mamaye yakin neman zaben sa.

Wasu tsofaffin dalibai ne dai suka gurfanar da shi a gaban kotu akan kaddarorin jami'ar sa wato Trump University.

A baya dai yayi ta nanata cewa shi ba zai biya komai ba amma a yanzu ya amince ya biya dala miliyan 25.

Mai shigar da kara a birnin New York ya bayyana matakin da cewa tamkar yin amai ne a lashe sai dai lauyan Mr Trump ya ce wannan ya nuna aniyarsa ta aje son kai gefe guda don tunkarar kalubalen da kasar ke fuskanta.