Kotu za ta yanke wa 'Hyena' hukunci cikin watannan

Mista Eric da ake wa lakabi da Kura
Bayanan hoto,

Iyayen 'yan matan da shugabanin al'umomi ke biyan Mista Eric kudi dan ya sadu da 'ya'yan na su

Babbar kotun kasar Malawi, ta samu mutumin da ya shaida wa BBC ya sadu da mata 104 alhalin yana dauke da cutar HIV ko Sida, da laifin yin lalata da yara. Kotun ta samu Eric Aniva da laifin aikata mummunar al'ada, da tilastawa amare da matan da mazajen su suka rasu yin jima'i.

A wata hira da ya yi da BBC gabannin yanke masa hukuncin, mista Eric ya kuma ce ya na wannan dabi'a ga kananan yara 'yan shekara 12, dan shiryawa lokacin budurcin su kamar yadda al'adar yankin da ya fito ta amince da yi.

Asirin Eric Aniva da ke wa lakabi da Kura ko Hyena a turance ya tonu ne, bayan wata hira da ya yi da BBC, inda ya bayyana aika-aikar da ya ke da sunan al'ada alhalin ya na dauke da cutar Kanjamau ba kuma tare da ya sanar da iyayen 'yan matan da matan da ke takaba ba.

Gwamnatin kasar Malawi ce da kanta ta bada izinin cafke Mista Eric, a wani mataki da ba a sabar ganin an dauka ba a kasar. kotun dai ta same shi da laifi karkashin dokokin Malawi da suka shafi Jinsi, cikin laifukan na sa akwai, yin lalata da kananan yara, da sunan mutunta al'ada, bayan wasu mata biyu sun shaidawa kotu cewa 'yan uwan su ne suka biya Mista Eric dan ya yi jima'i da wasu kananan yara alhalin ya na dauke da kwayar cutar HIV.

Batun aika-aikar da Mista Eric ya yi dai ya ja hankalin kasashen duniya, an kuma yi zazzafar muhawara a ciki da wajen kasar kan ci gaba da yin wannan mummunar al'ada ko kuma gwamnati ta soke ta baki daya.

A ranar 22 ga wannan watan ne za a yanke masa hukuncin da ya dace da laifin da ya aikata.