An kawo karshen dokar ta baci kan Zika- WHO

Jaririya da aka haifa da cutar Zika
Bayanan hoto,

Cutar Zika na yi wa jarirai illa tun a cikin iyayensu

Hukumar lafiya ta duniya ta janye dokar ta bacin da aka ayyana akan cutar Zika saboda a yanzu an shawo kan matsalar.

Duk da wannan sanarwa, ma'aikatar lafiya ta kasar Brazil ta ce za ta ci gaba zage dantse dan magance cutar saboda irin illar da ta ke yiwa jarirai a cikin mahaifiyarsu.

Brazil dai na daga cikin kasashen da cutar Zika ta fi yaduwa tsakanin mata masu juna biyu, wadda ke janyo haifar jarirai da tawaya a kwakwalwarsu da dan karamin kai.

Likitocin sun bayyana cutar a matsayin annoba, kuma wasu sun shawarci mata a kasashen da cutar ta bulla, da su jinkirta daukan ciki.

A kwanakin baya ne wasu kwararru a kan kiwon lafiya daga Amurka da kasashen Latin Amurka da Karebiyan fiye da talatin, suka yi taron koli na farko a kan yadda za a tunkari cutar ta Zika.

Masana kimiyya da Kungiyar lafiya ta Duniya- WHO, na ganin sauron da ke dauke da cutar ne ake alakantawa da cutar da haddasa haihuwar gilu.