'Yan kasar na kiran Firaiminista Razak ya sauka

Najib Razak

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Badakalar kudaden dai ta janyowa Mista Razak bakin jini a kasar

Jami'an 'yan sanda a kasar Malaysia sun tare wasu manya hanyoyi a Kuala Lumpur babban birnin kasar, gabanin fara wani gangami da masu rajin kare demukradiya suka shirya.

An dai shirya yin zanga-zanga kan kiraye-kirayen da ake ta yi ga Firaiministan kasar Najib Razak ya yi murabus kan zargin da ake masa da hannu a wata badakala ta makuden kudade.

Ya kuma musanta zargin, sai dai masu fafutika a kasar sun ce yana yiwa masu sukarsa bazarana.

An tsare wasu shugabannin adawa a kasar yayin da 'yan sanda suka ce zanga-zangar da aka shirya gudanarwa a yau din nan haramtacciya ce.