Guardiola ya ce yin jam'i yana kara wa 'yan wasa kuzari

Guardiola ya ce, "ba zai yiwu dan wasa ya murza leda da kyau ba idan ba ya jima'i da matarsa."

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Guardiola ya ce, "ba zai yiwu dan wasa ya murza leda da kyau ba idan ba ya jima'i da matarsa."

Kocin Manchester City Pep Guardiola ya musanta rahotannin da ke cewa yana hana 'yan wasan kungiyar yin jima'i da daddare.

Dan wasan tsakiya na kungiyar Samir Nasri, wanda ya tafi Sevilla a matsayin aro, ya yi zargin cewa Guardiola ya haramta wa 'yan wasa yin jima'i a lokacin ne domin "su rika samun isasshen bacci da daddare".

Amma tsohon kocin na Barcelona, mai shekara 45, ya musanta zargin inda ya ce yana karfafa gwiwar 'yan wasansa su rika yin jima'i a kai-a kai.

Guardiola ya ce, "Ba zai yiwu dan wasan ya murza leda da kyau ba idan ba ya jima'i da matarsa."

Kocin dai ya hana Nasri yin atisaye tare da takwarorinsa na kungiyar gabanin kakar wasa ta bana saboda ya ce ya yi kiba sosai.

Ya shaida wa wani shirin gidan talabijin na Faransa mai suna L'Equipe du Soir cewa Guardiola "yana son 'yan wasansa su kasance sirara kuma masu kuzari" kuma ya yi ikirarin cewa Guardiola ya gaya wa Lionel Messi zai kaucewa fuskantar tsamin jiki idan ya daina yin jima'i da daddare.

Sai dai Guardiola ya ce: "Ban taba haramta wa 'yan wasa yin jima'i ba kuma ba zan taba hana su ba. Idan dan wasa yana yin jima'i ya fi kuzari."

Rahotanni na cewa Guardiola ya hana yin amfani da wi-fi a wajen yin atisaye domin ya karfafa dankon zumunci tsakanin 'yan wasa, yayin da dan wasan baya Gael Clichy ya ce an hana 'yan wasan cin pizza, da lemon kwalaba da nau'in abinci mai nauyi.