'Yan sanda sun ce sun kama makaman 'yan Shi'a a Kano

'Yan sanda sun ce 'yan Shi'a na son tayar da hankali

Asalin hoton, NIGERIA POLICE

Bayanan hoto,

'Yan sanda sun ce 'yan Shi'a na son tayar da hankali

Rundunar 'yan sandan jihar Kano da ke Najeriya ta ce ta kama wata babbar mota dauke da makaman `yan kungiyar `yan uwa musulmi.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kano, Magaji Musa Majiya ya shaida wa manema labarai ranar Juma'a cewa motar tirelar tana kan hanyarta ne daga Yobe zuwa Zaria, inda 'yan Shi'a za su yi gangamin tunawa da ranar Arba'in.

Kokarin da muka yi domin jin martanin 'yan Shi'ar bai yi nasara ba domin mun kira lambar kakakin kungiyar amma ba ta shiga ba, kuma mun aika masa sakon tes bamu samu amsa ba.

Amma a baya kungiyar ta sha musanta cewa tana neman tayar da rigima.

A bangaren 'yan sanda, Magaji Musa Majiya ya ce, "A ci gaba da binciken da muke yi kan hatsaniyar da aka yi tsakanin 'yan sanda da 'yan Shi'a ranar 14 ga watan Nuwamba a kan hanyar Kano zuwa Kaduna, mutanen da muka kama bisa zargin tayar da rigimar sun shaida mana cewa suna da motar tirela mai dauke da makamai, wacce ta nufo Kano inda za su taru zuwa Zaria.

"Nan da nan jami'anmu suka shiga aiki, inda sojoji suka kama tirelar a wani wajen binciken abubuwan hawa, sannan suka mika ta ga 'yan sandan Yobe, wadanda su kuma suka mika wa jami'anmu domin ci gaba da yin bincike."

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kanon ya kara da cewa an tafi da mutanen da ake zargin wajen motar, kuma da aka yi bincike a cikinta an samu wasu kwari da baka, da rodina da duwatsu da dankuna da injin janareta da tutoci da kayan abinci.

A cewarsa, hakan ya nuna cewa kungiyar ta 'yan Shi'a tana son tayar da zaune tsaye kuma hukumomi ba za su bar ta ta yi abin da ta ga dama ba.

Asalin hoton, Nigeria police

Bayanan hoto,

Za a ci gaba da gudanar da bincike

Amurka ta bukaci a yi taka-tsan-tsan

Hakan na faruwa ne kwana guda bayan gwamnatin Amurka ta nuna damuwa game da asarar rayukan da ake yi a Najeriya, sakamakon arangama tsakanin `yan kungiyar `yan uwa musulmi da jami`an tsaro.

Wata sanarwa da ofishin jakadancin kasar da ke Najeriya ya fitar, ta ce akwai bukatar a dinga samun fahimtar juna tsakanin mabiya kungiyar da kuma mahukunta a Najeriya.

Amurka ta ce artabun da aka yi tsakanin `yan sanda da `yan Shi'a, wadanda ke tattaki daga Kano da nufin zuwa birnin Zazzau, a makon jiya, abin takaici ne.

Amurka ta ce hankalinta ya tashi matuka da irin karfin da `yan sanda suka yi amfani da shi a karawar, duk cewa mahukunta a Najeriya na ci gaba da gudanar da bincike a kan lamarin.

Gwamnatin Amurkar ta bukaci `yan kungiyar da kuma bangaren gwamnatin Najeriya da su kai zuciya nesa, tare da mai da hankali wajen tuntubar juna da nufin samun maslaha.

Sanarwar ta kara da cewa `yan kungiyar `yan uwa musulmi suna da `yancin yin taro da sauran hidimominsu na addini, kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadar, amma a bangare guda kuma wajibi ne su kasance masu martaba dokar kasar.