An yi wa sabon mataimakin shugaban Amurka a-ture

Jami'an tsaro sun sa ido sosai a wajen taron

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Jami'an tsaro sun sa ido sosai a wajen taron

An yi wa Mike Pence, mataimakin zababben shugaban Amurka Donald Trump, eho a wurin wani bikin al'adu da aka yi ranar Juma'a a birnin New York.

Bayan an gama bikin ne, daya daga cikin mutanen da suka hada shi ya mike ya yi godiya ga Mr Pence saboda halartar taron sannan ya karanta masa wata wasika.

Brandon Dixon said ya ce, "Yallabai, mu Amurkawa ne da muka fito daga kabilu da addinai daban-daban amma muna dari-darin saboda gwamnatinku ba za ta yi mana adalci ba."

Mahalarta taron sun yi ta jinjinawa Dixon bayan ya yi wannan korafi.

Rahotanni na cewa mutanen da suka hada bikin ne suka marubuta wasikar bayan sun fahimci cewa Mr Pence zai halarci wajen taron.

An yi ta yi wa Mr Pence eho da karfi a lokacin da ya shiga wajen bikin, kuma wani mutum da ya halarci taron ya ce sai da aka tsayar da yin jawabai saboda girman ehon da aka yi masa.

Sabon mataimakin shugaban kasar ya jawo ce-ce-ku-ce a farkon wannan shekarar bayan ya sanya hannu kan wata doka da ta hana auren jinsi daya, kodayake daga baya ya yi wa dokar gyaran-fuska.