Ana ci gaba da zaman dar-dar a Congo

Congo

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Jinkirta zabe da aka yi ya na ci gaba da haifar da zaman dar-dar a Jamhoriyar Dimukradiyar Congo

Rahotanni daga Jamhoriyar Dimukradiyar Congo na cewa ana zaman dar-dar a kasar, inda aka girke jami'an tsaro a Kinshasa babban birnin kasar, bayan hukumomi sun hana gudanar da wani gangami na 'yan adawa.

Wadanda suka shaida lamarin sun ce an hana jami'an Majalisar Dinkin Duniya tunkarar gidan madugun 'yan adawa, Etienne Tshisekedi.

Mista Tshisekedi ya yi kira ga shugaban kasar Joseph Kabila da ya sauka daga kan mulki bayan wa'adinshi ya cika a karshen watan Disamba.

Mista Kabila ya ce wajibi ne a dage zaben watan gobe zuwa shekara mai zuwa saboda dalilai na kayan aiki.

A halin yanzu, shugaba Kabila ya sanar da sunan Samy Badibanga, wani dan majalisar dokoki na bangaren adawa a matsayin sabon Firayiministan kasar.