Saudiya ta dakatar da bude wuta a Yemen na sa'o'i 48

Yemen

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

'Yan tawayen Houthi sun amince da yarjejeniyar tsagaita wutar

Rundunar dakarun kawance da Saudiya ke jagoranta dake taimaka ma gwamnatin Yemen yaki da 'yan tawayen Houthi, ta sanar da dakakar da bude wuta na sa'o'i arba'in da takwas.

Saudiya ta ce za a tsawaita yarjejeniyar idan har 'yan tawayen, da masu mara musu baya suka mutunta ta, ta hanyar bari akai kayan agaji yankunan da aka yi wa kawanya, da suka hada da birnin Taez.

Suma 'yan tawayen sun nuna a shirye suke su yi aiki da yarjejeniyar wacce ta fara aikin da tsakar rana a kasar.

Sai dai kuma, bayan 'yan sa'o'i da fara aiki da yarjejeniyar, an samu rahotanni dake cewa ana ci gaba da bata kashi.

Fiye da mutane dubu goma ne suka mutu a yakin da aka shafe watanni ashirin ana yi a kasar.

A farkon wannan makon, Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya ce rundunar dakarun kawancen da 'yan tawayen Houthin sun amin ce yarjejeniyar ta fara aiki tun daga ranar Alhamis.

Sai dai gwamnatin kasar da kasashen duniya suka amince da ita, karkashin jagorancin shugaba Abdrabbuh Mansour Hadi dake gudun hijira, ta ki amincewa da ita, tana mai cewa ba a sanya ta a ciki ba.