MDD: Yau ce ranar yaki da cin zarafin kananan yara

Save the Children

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Save the Children ta ce miliyoyin yara a kasashen duniya na fama da cin zarafi a kowacce shekara

Yau ce ranar da majalisar dinkin duniya ta ware don fadakar da kasashen duniya kan bukatar hadin kai da ingantya rayuwar kananan yara a fadin duniya.

Ranar 20 ga watan Nuwambar ko wace shekara muhimmiyar rana ce da taron kolin shekara ta 1959 na Majalisar Dinkin Duniya ya ayyana kudirin kare hakkin kananan yara.

A kuma irin wannan rana ne a shekarar 1989 kwamitin Majalisar Dinkin Duniya ya tabbatar da kudurin dokar kan cin zarafin yara.

Take ranar ta yau shi ne Kawo karshen cin zarafin yara, kamar yadda asusun yara na majalisar dinkin duniya ya bayyana, a ko wace shekara miliyoyin yara a fadin duniya za su fuskanci matsalili na cin zarafi mai nasaba da tashe-tashen hankula.

Kananan yara a ko wace kasa, a ko wane bangare na al'umma na fuskantar musgunawa da cin zarafi iri daban-daban.

Ire-iren cin zarafin na faruwa ne a gidaje, da makarantu,da wuraren aiki, da kuma wuraren da ake fama da yake-yake, da abkuwar bala'oin da suka shafi muhalli.

Harwayau yawancin cin zarafin da ake yiwa yara da suka hada da ba su horon da ya fi karfin su a lokacin da suka yi laifi, misali sanya su aikin karfi da sauran su, kuma a wasu kasashen ba a cika kallon irin hakan ba a matsayin cin zarafin yara.

Wani abun damuwa game da cin zarafin yara da ba kasai ake ganin shi haka ba shi ne yiwa yara mata auren wuri, da yi musu kaciya, safarar yara kanana dan yin aikatau a birane ma na daga cikin matsalolin da yara ke fuskanta, akan kuma tilasta musu shiga aikin soja musamman a kasashen da ake fama da yake-yake.

Bincike ya gano cewa matsalolin cin zarafin da yara kanana ke fuskanta na dakushe musu rayuwa, da janyo musu tsangwama a cikin al'uma da sauran su.

Kungiyar bada agajin ta Save the Children na kokarin ganin ta magance matsalolin da yaran ke fuskanta, da tabbatar da an tallafawa wadanda suka samu kan su cikin halin domin inganta rayuwarsu, da kwato musu hakki idan bukatar hakan ta taso.