Sama da mutum 100 ne suka mutu a hatsarin jirgin ƙasa a Indiya

Hadarin jirgin kasa a India

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ana yawan hadarin jirgin kasa a India

'Yan sanda sun ce sama da mutum 100 ne suka mutu yayin da fiye da mutum 150 suka jikkata a wani hadarin jirgin kasa da ya abku a arewacin India.

Jirgin da ke zirga-zirga tsakanin manyan birane ya taso ne daga birnin Indore da ke tsakiyar kasar zuwa birnin Patna da ke gabashin kasar lokacin da ya kauce daga layin dogo kusa da garin Kanpur.

Masu bayar da agaji sun yi ta kustawa cikin taragwan jirgin suna cire mutane.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Mutane da dama sun jikkata

Har yanzu ba a san abin da ya yi sanadin hatsarin jirgin ba.

Daya daga cikin fasinjojin jirgin, Krishna Keshav, ta shaida wa BBC cewa: "Mun farka daga bacci a firgice da kimanin karfe uku na dare. Taragwai da dama na jirgin sun kauce daga layin dogo lamarin da ya jefa kowa cikin dimuwa. Na ga gawarwakin mutane da dama da kuma mutanen da suka jikkata."

Ministan zirga-zirgar jiragen kasa na India ya bayar da umurnin a gudanar da bincike a kan hadarin.