Facebook zai magance matsalar wallafa labaran bogi

Mark Zuckerberg

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ko a lokacin zaben Amurka an soki shafin na Facebook

Kamfanin Facebook ya sanar da wasu sabbin matakai na rage yawan labarai na bogi da ake wallafawa a shafin sa.

A wani sako daya wallafa, shugaban kamfanin Mark Zuckerberg ya ce Facebook na bullo da wasu sabbin hanyoyi tantance labarai na bogi inda yake duba yiwuwar kafa wata hukuma ta tantance labarai na gaskiya.

Facebook dai ya yi ta shan suka akan yawan labarai na bogi da aka rika wallafawa a shafin sa gabannin zaben Amurka wanda ake zargin cewa, irin labaran da aka rika wallafawa sun taimaka kan yadda sakamakon zaben ya kasance.

A ranar asabar ne Mr Zuckerberg ya yi jawabi ga shugabannin kasashen duniya dake halartar taron APEC a Peru, inda ya bukace su da su yi aiki tare wajen ganin an hada duniya wuri guda ta fuskar samar da hanyoyin Internet don magance talauci tsakanin mutane biliyan 4 da basu da damar amfani da Internet.