Labari kan matsalolin da auren dole ke janyo wa

A ci gaba da karanto muku gajerun labarai ukun da suka yi nasarar lashe gasar BBC Hausa ta farko ta rubutun kagaggen labari ta mata zalla, a yau za mu kawo muku karatun labarin "In Da Rai".

Wannan labari ne dai ya zo na uku a gasar.

Baya ga ukun da suka fi fice kuma, sannu a hankali za mu kawo muku wasu labaran 12 wadanda alkalan gasar suka zaba a matsayin wadanda suka cancanci yabo.

Ga dai Amina Gambo Adam Kwaru, marubuciyar In Da Rai: