Bajintar da Ronaldo ya sake yi ta ƙara wa Real Madrid martaba

Ronaldo

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Ronaldo ya fi kowanne dan wasan La Liga yawan kwallayen da aka ci ta bugun firi-kik

Kwallo uku da Cristiano Ronaldo ya zura shi kadai a karo na 39 sun bai wa Real Madrid karin damar ci gaba da zama ta daya a saman tebirin gasar La Liga bayan sun doke Atletico da ci 3-0.

Dan wasan gaban na Portugal ya soma zura kwallo ne bayan an jefo kwallo daga bugun firi-kik inda ya bai wa golan Atletico Jan Oblak kafa.

Ronaldo ya kara kwallo ta biyu daga wurin bugun fenareti, inda kuma ya cike kwallo ta uku bayan ya samu kwallon da Gareth Bale ya mika masa.

Yanzu dai Real suna kan gaban Barcelona, wacce ita ce ta biyu, da maki hudu bayan da suka tashi babu ci a wasan da suka yi da Malaga.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Har yanzu Ronaldo bai nuna alamar gajiyawa ba

Ronaldo ya zura kwallo takwas a gasar La Liga ta bana, inda ya yi kankankan da Lionel Messi da Luis Suarez.

Kwallo ukun da dan wasan mai shekara 31 ya zura sun sa ya fi shahararren dan wasan Real din nan Alfredo Di Stefano, wanda ya zura ci 17, yawan kwallaye da guda daya a wasannin da Madrid ta fafata.