Man Utd ta fi kowacce kungiya a Premier rashin sa'a - Mourinho

Asalin hoton, Getty Images
Mourinho ya ce Arsenal ta yi nasara a kansu
Kocin Manchester United Jose Mourinho ya ce su ne suka fi kowacce kungiyar da ta shiga gasar Premier rashin sa'a.
United ta gaza yin nasara a kan Arsenal a Old Trafford bayan da a minti na 89 Olivier Giroud ya farke kwallon da Juan Mata ya zura inda suka tashi da ci 1-1.
Yanzu dai United a wasa daya kawai ta yi nasara cikin wasan Premier shida da suka yi a bana.
Mourinho ya ce: "Ba zan dora laifi kan 'yan wasana ba, amma dai abin takaici ne domin kuwa a ganina mun sha kaye yayin da Arsenal suka yi nasara."
Ya kara da cewa: "Idan muka mayar da hankali wajen yin kunnen-doki da Burnley, Stoke da kuma Arsenal - za mu samu maki tara cikin sauki. Idan da a ce mun samu karin maki shida da mu ne na hudu a saman tebirin Premier, kuma kusa da na zama na daya."
United ta ci gaba da zama a mataki na shida a tebirin gasar, inda take bayan Arsenal, wacce take matsayi na hudu, da maki shida, wadanda su kuma ke bayan ta daya Liverpool da maki biyu.