'Yan sanda sun kashe mayakan Al Shabab 4 a Kenya

al shabab

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Mayakan Al Shabab suna da alaka da kungiyar Al Qaeda

Hukumomi a Kenya sun ce 'yan sanda sun kashe wasu da ake zargi 'yan bindiga masu tsananin kishin Islama ne su hudu a kusa da iyakar Somaliya.

Kwamishinan 'yan sanda na Mandera ta Kudu, Fredrick Shisia ya ce 'yan bindigan sun yi niyyar kai hari ne kan wani ofishin 'yan sanda.

Ya ce 'yan sanda sun samu rahoton cewa 'yan bindigan sun tsallaka zuwa cikin Kenya ta yankin Elwak, abin da yasa jami'an tsaro suka bazama don fatattakarsu.

Ya ce cikin kayayyakin da aka kwace daga hannun 'yan bindigan, akwai bindigogi, da wayoyin salula da kakin sojin Somaliya.

Mista Shisia ya ce 'yan bindigan suna boyewa ne a Qoble, da nufin kai hari kan motocin safa dake bin hanyar.

Rahotanni sun ce 'yan bindigan suna cikin mambobin kungiyar Al Sabab ashirin da suka sha alwashin daukar fansa akan Kenya, saboda girke dakarunta da ta yi a Somaliya.

A cikin makon daya gabata ma, 'yan sanda sun harbe wani da ake zargi dan kungiyar Al Shabab ne a yankin.