'Yan bindiga sun halaka sama da mutane 40 a Zamfara

Nigerian soldiers

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Jami'an tsaron Najeriya dake yaki da 'yan bindiga

A jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya, wasu 'yan bindiga sun sake kai hari a wasu kauyuka a karamar hukumar Zurmi, inda wasu rahotanni ke cewa sun kashe mutane kimanin 44.

Harin wanda aka kai a ranar Asabar da daddare ya faru ne kwana daya bayan an kashe wasu mutane tare da sace wasu da dama, a wani harin na daban da aka kai a kan wasu kauyuka a yankin.

Wasu rahotanni sun ce kimanin mutane dubu daya ne suka tsere daga kauyukan domin tsira da rayukansu.

Rahotannin sun ce 'yan bindigar sun isa kauyukan Tubali da Daular Moriki ne a kan babura masu yawa, inda suka rika harbin kan-mai-uwa-da-wabi.

A ranar Alhamis da ta wuce ne aka yi garkuwa da sama da mutane 40 da suke kan hanyarsu ta zuwa cin kasuwa.

Yayin da wasu rahotanni suka ce a ranar Juma'a kuma, 'yan bindiga sun je garin Sabon Gida, inda suka rika tambayar a nuna musu wani shugaban 'yan sintiri masu aikin sa-kai.

Rashin ganin shugaban 'yan sintirin ne ya sa suka fara rikici da jama'ar kauyen, tare da taimakon mutanen wasu kauyuka da ke kusa.

Mutane tara ne aka kashe a rikicin, ciki har da 'yan bindigar su biyu.

Ana ganin wannan ne ya sa 'yan bindigar yin zuga zuwa kauyukan da ke karamar hukumar Zurmi, domin ramuwar gayya.

A lokacin hada wannan rahoto dai, Kakakin rundunar 'yan sandan jihar ya ce suna tattara bayanai tukunna, kafin su ce wani abu a kai.