Ana neman wadanda suka sace tsohon ministan Nigeria

Nigeria police

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Batun sace mutane ya zama ruwan-dare a jihar Kaduna

'Yan sanda a Nigeria na ci gaba da farautar wadanda suka sace Tsohon Ministan kasar, Ambassada Bagudu Hirse, a wani hari a gidan sa da ke garin Kaduna.

Rahotanni na cewa 'yan bindigar sun kai hari a gidan ne da yammacin Lahadi, inda suka yi musayar wuta da masu gadin gidan.

Rundunar 'yan sandan jahar Kaduna ta tabbatar da lamarin.

Kakakin rundunar, ASP Aliyu Usman ya ce duk da cewa ba a kama ko daya daga maharan ba, jami'an 'yan sanda sun baza komar su domin gano wadanda suka sace tsohon ministan.

Sace sacen jama'a don neman kudin fansa dai na ci gaba da zama wata babbar matsala a jahar Kaduna.

A kwanakin baya, wasu 'yan bindiga sun sace tsohuwar ministar Muhalli Laurantia Malam tare da mijin ta Mista Pious Malam, haka kuma a makon da ya gabata ne aka sace wani babban jami'i kungiyar Jama'atul Nasrul Islam tare da direban sa a hanyar su ta zuwa Kaduna daga garin Jos babban birnin jahar Pilato.

A watan Yulin da ya gabata ma, an sace jami'in jakadancin Saliyo, Manjo Janar Nelson Williams ko da yake an sako shi bayan kwashe kwanaki a hannun wadanda suka sace shi.