'Mun karya lagon Boko Haram'- Sojin Nigeria

Sojojin Najeriya dake yaki da Boko Haram a Maiduguri

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Sojojin Najeriya dake yaki da Boko Haram a Maiduguri

A Nigeria, rundunar sojin kasar ta musanta cewa ta rage yawan sojojinta a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Rundunar sojin na mayar da martani ne akan fargabar da wasu mazauna birnin Maiduguri ke yi cewa, karuwar hare-haren kunar bakin wake daga 'yan kungiyar Boko Haram yasa gwiwar su ta yi sanyi.

A wata hira da BBC wasu mazauna birnin Maiduguri sun bayyana cewa matakin rage sojojin ya taimaka wajen karuwar hare-hare kunar bakin wake da ake fuskanta a jihar tare da haifar da fargaba.

Sai dai kakakin rundunar sojin kasa ta Nigeria Kanar Sani Usman Kukah Sheka ya ce bai kamata ba wasu jama'a su rika cewa ana cikin fargaba a birnin Maiduguri, inda ya nanata cewa sojojin kasar sun karya lagon Boko Haram.