An bude kasuwar baje-koli a Kano

Jihar Kano ce cibiyar kasuwancin arewacin Nigeria
Bayanan hoto,

Jihar Kano ce cibiyar kasuwancin arewacin Nigeria

Kasuwar baje-kolin duniya ta Kano ta fara ci a karo na 37.

Rahotanni sun ce tuni 'yan kasuwa a ciki da wajen Nijeriya suka fara baza hajar su.

Baje-kolin dai na zuwa ne a lokacin da al'ummar kasar ke kokawa a kan hauhawar farashin kayayyaki da matsin tattalin arziki.

Sai dai duk da haka, kasuwar wadda cibiyar bunkasa ciniki, masana'antu, ma'adanai da aikin gona ta jihar Kano ta shirya, na jan hankalin masu saye da sayarwa.