Za a tafi zagaye na biyu a zaben fidda gwani

Francois Fillan

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Tsohon Shugaban Fransa Nicolas Sarkozy ya sha kaye a zaben na farko, ya kuma nuna goyon baya ga Mista Fillon

Tsofaffin Firaiministan kasar Faransa biyu za su fuskanci juna a zaben fidda gwani zagaye na biyu na tsayar da dan takara a zaben shugaban kasar da za'a gudanar shekara mai zuwa.

Francois Fillon da kuma Alain Juppé sun zo na daya da na biyu ne a zagayen farko na zaben da jam'iyyar Republican ta shirya.

Tsohon shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy ya sha kaye tun a zagayen farko ne bayan da ya zo na uku, kuma yana daya daga cikin 'yan takaran da suka sha kaye a zagayen farko daya nuna goyon bayan sa ga Mr Fillon a zaben fidda gwanin da za'a gudanar ranar Lahadi mai zuwa.

Wakilin BBC yace wannan zabe yana da matukar muhimmanci saboda duk wanda ya lashe shi akwai yiwuwar shi ne zai zama sabon shugaban kasar Faransa.