Al'ummar kasar Mali na dakon sakamakon zabe

Masu kada kuri'a a wurin zabe

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

'Yan adawa sun soki shugaba Keita saboda barin yin zabe a arewacin kasar, da yawancin mutanen yankin na sansanin 'yan gudun hijira

An gudanar da zabe a kasar Mali wanda shine zabe na farko da aka yi tun shekarar 2013 bayan an yi ta dagewa har sau hudu saboda rashin tsaro.

Sai dai yayin da rahotanni ke cewa zaben ya gudana cikin kwanciyar hankali a kudancin kasar, an soke zaben ne a wasu yankuna bakwai dake arewaci wadanda kungiyoyin masu fafutukar Islama suka kwace iko lokacin da 'yan tawaye suka yi bore shekaru hudu da suka gabata.

Jam'iyyun adawa da wasu kungiyoyin dai sun soki gwamnatin shugaba Ibrahim Boubakar Keita da shirya zabe a arewacin kasar duk kuwa da cewa jama'a da dama a yankin na zaune ne a sansanonin 'yan gudun hijira.

Kawo yanzu dai ba'a fitar da sakamakon zaben ba.